<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>349</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) A cikin mugunta an yi cikina
 A ciki kuwa uwata ta haife ni.
 Ҡamnar Yesu ta zo ta neme ni
 Har ta bayyana mani dukan laifina.

[V2]
 KORUS
 Musulmi da arna duk
 Ku tuba tun yanzu
 Gama ba daman tuba ranar shari'a.

[V3]
 2) Gama Yesu shi ba ya zaɓe ba
 Baƙi, fari, ko kuwa rawaya ne
 Ya mai da mu duka abokansa
 Gama shi ba ya mai da kansa ya fi kowa.
 Korus

[V4]
 3) Ekklisiya , mu ɗauki bishara,
 Mu shiga cikin dukan ƙauyekan
 Ga yamma suna ta mutuwa
 Bari mu bar gida mu je, mu bishe su.
 Korus

[V5]
 4) Ҡamnar Yesu ba za ta ƙare ba
 Har wa yau ma tana a duniyan nan.
 Domin ta ba mu Ruhu Mai Tsarki
 Har shi taimake mu a cikin aikinsa.
 Korus

[V6]
 5) Ku masu bi, mu yabi Mai Ceto
 Mu shaida sunansa ga mutane
 Mu yi ta ce, &quot;Ga hanya zuwa rai
 Gama ba wata hanyar ceto sai Yesu&quot;.
 Korus</lyrics>
<title>A Cikin Mugunta An Yi Cikina LW349</title>
</song>